Ginola na son zama shugaban FIFA

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ginola na bukatar goyon bayan hukumomin kwallon kafa biyar

Tsohon dan wasan Faransa, David Ginola, zai shiga takarar neman shugabancin hukumar kwallon kafar duniya, FIFA.

Ana sa ran zai sanar da bukatarsa ta neman shugabancin hukumar a wani taron manema labarai da zai yi nan gaba kadan a birnin London.

Ginola zai fafata da Yarima Ali Bin Al Hussein na Jordan, da wani dan kasar ta Faransa, Jerome Champagne da kuma shugaban hukumar Sepp Blatter, wajen neman shugabancin hukumar.

Babu dai tabbas ko Ginola zai iya yin takarar domin yana bukatar goyon bayan hukumomin kwallon kafa guda biyar.

Wakilin BBC ya ce takarar da Ginola zai yi alama ce da ke nuna cewa akwai bukatar sauyi a hukumar bayan ta yi fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa a 'yan shekarun nan.