Bam ya hallaka mutane a Gombe

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Harin bam a tashar Dukku ta Gombe

Rahotanni daga Gombe da ke arewa maso gabashin Nigeria na cewa bam ya fashe a unguwar arawa ta birnin.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Sai dai bayanai sun ce bam din ya fashe ne da misalin karfe bakwai na yamma.

Wannan ne karo na biyu cikin mako guda da bam ya fashe a garin Gombe.

Wurin da bam din fashe akwai hada-hadar jama'a sosai.

A karshen watan Disamba ma mutane a kalla 20 ne suka rasu sannan fiye da 40 suka jikkata sakamakon tashin bam a wata tashar mota a Gombe.