Ba siyasa ce ta kai ni Borno ba - Jonathan

Hakkin mallakar hoto State house
Image caption Jonathan ya kwashe kusan shekaru biyu bai kai ziyara Borno ba duk da kashe-kashen da ake yi wa mazauna jihar.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce ba sha'anin siyasa ne ya sa ya kai ziyara birnin Maiduguri na jihar Borno ba.

Kakakin shugaban, Reuben Abati ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa mutanen da suka ce shugaban ya kai ziyarar ce kawai domin neman a sake zabensa shirme kawai suke yi.

A cewarsa, "duk jawaban da shugaban ya yi a Maiduguri babu kalma guda daya ta siyasa.Shugaban bai tattauna da kowa kan siyasa ba; don haka masu cewa ya je ne domin siyasa sun yi hakan ne don shafa masa kashin kaji"

Ziyarar da shugaban ya kai ranar Alhamis dai ita ce ta farko cikin kusan shekaru biyu, duk da cewa ana ci gaba da kashe mutane a jihar.