Siyasa ce ta kai Jonathan Borno - Kwankwaso

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Jonathan bai kai ziyara jihar ba duk da kashe-kashen da ake yi wa mutane sai yanzu

Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya Rabi'u Kwankwaso ya ce shugaba Goodluck Jonathan ya kai ziyara Maiduguri ne domin yakin neman zabe.

A wata hira da ya yi da BBC, gwamna Kwankewaso ya ce abin takaici ne cewa duk da kashe-kashen da aka kwashe tsawon lokaci ana yi a jihar ta Borno, shugaba Jonathan bai kai ziyara ba sai yanzu da yake neman a sake zabensa.

A cewarsa gwamnan, kowa ya san cewa Mr Jonathan ya kai ziyarar ce ba domin ya jajantawa mazauna jihar ba, kamar yadda shugaban ya yi ikirari.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ya kai ziyara a yankin tun daga watan Maris na shekarar 2013.

'Yan kasar dai sun yi ta sukan shugaban musamman bayan da ya ki kai ziyara a jihar lokacin da aka sace matan makarantar Chibok fiye da 200, a watan Aprilun 2014.

A baya bayan nan ma shugaban bai ce komai ba duk da kisan da 'yan Boko Hrama suka yi wa mutane sama da 2000 a garin Baga.