Merkel ta ce za a koma sa-ido a intanet

Sugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana samun karuwar masu tada kayar baya da ke amfani da shafukan internet wajen yada manufarsu.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce nan ba da jimawa ba za ta matsawa tarayyar turai lamba a kan komawa tsarin rike bayanan intanet domin yakar 'yan ta'adda.

A watan Aprilun shekarar 2014 ne kotun kolin Turai ta yanke tsarin da ake amfani da shi na nadar bayanan da bai dace ba.

A shekarar 2006 ne aka fito da tsarin da zai ba wa 'yan sanda damar sanya idanu kan 'yan gwagwarmaya ta hanyar bayanan sirrinsu na Internet.

Miss Merkel na wannan jawabi ne a gaban majalisar dokokin Jamus, a kokarin daukar matakan hana faruwar harin da wasu masu kishin Islama suka kai a gidan mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo a kasar Faransa inda mutane 17 suka rasa rayukansu, a makon da ya wuce.

A shekarar da ta gabata kasar Jamus ta tsaurara matakan Internet a kasar, bayan kwarmata bayanan da Edward Snowden ya yi kan cewar Amurka na nadar bayanan sirri wasu daga cikin shugabanni ciki har da Miss Merkel.