Bayanai kan dan Saudiyyar da aka yi wa bulala

Shin wa ye Raif Badawi kuma me ya sa gwamnatin Saudiyya ta yi masa bulala a bainar jama’a? Ana sa ran Raif Badawi zai sha bulala 50 a kowane mako a cikin makonni 20. Menene laifinsa kuma me ya sa ake hukunta shi- kwararru sun ce hukuncin ya wuce gona da iri. Ga ga karin bayani.

Wa ye Raif Badawi?

 • Raif Badawi, mai shekaru 31, dan kasar Saudiyya ne mai rubutu a shafin intanet wanda ke son a dunga mahawara a kan harkokin addinni da na siyasa a Saudi Arabia a shekara ta 2008.
 • A shekarar 2012, an tsare shi a Jeddah inda aka tuhume shi da sukar Askarawa da malaman Saudiya.
 • A shekarar 2013, an yanke wa Mr Badawi hukunci a kotu.
 • A ranar Juma’ar da ta gabata aka yi masa bulala 50 a bainar jama’a a Jeddah.
 • A wannan makon aka dage yi masa bulala saboda rashin lafiya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Badawi tare da iyalansa

Me ye laifinsa?

 • Shafin intanet na Mr Badawi na kakkausar suka a kan hukumomin addinni a Saudiyya, abin da ya janyo aka yi kokarin hallaka shi a 2012, har ya kai ga matarsa da iyalansa suka nemi mafakar siyasa a kasar Canada.
 • Hakan ya biyo bayan fatawar da wani malamin addinni Sheikh Abdulrahman al-Barrack ya yi cewa Mr Badawi “ba Musulmi ba ne” kuma “ya yi ridda”. A cewarsa, Mr Badawi ya ce “Musulmi da Yahudawa da Kiristoci da marasa addinni duka daya suke”.
 • An tuhumi Mr Badawi da “batanci ga Islama” kuma “ya nuna rashin da’a”.
 • A 2008, na zarge shi da yin ridda- abin da hukuncin kisa ne , amma daga bisani aka janye tuhumar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matar Badawi ta koma Canada a shekarar 2012

Shin hukuncin ya yi tsauri?

 • Da farko an yanke wa Mr Badawi hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari da kuma bulala 600.
 • Daga bisa ni aka kara ya zama bulala 1000 da daurin shekaru 10.
 • A bainar jama’a aka yi masa bulala, watau za a dunga yi masa bulala 50 da dorina a duk ranar Juma’a na tsawon makonni 20.Farfesa Madawi al-Rasheed na jami’ar London School of Economics ya bayyana hukuncin da cewar ya yi tsauri.
 • Mutane a shafukan zumunta na zamani a Saudiyya sun ce hukuncin ya yi daidai.

Me kasashen duniya suka ce ?

 • Kasashen da ke yammacin duniya kamar Amurka da Canada da Jamus da kuma Norway sun ce hukunci a kan Mr Badawi bai yi daidai ba.
 • A ranar Laraba, ministan harkokin wajen Canada John Baird ya ce ‘hukuncin ya taka ‘yancin dan adam’.
 • Matar Mr Badawi, Ensaf Haidar ta ce “Ina kira ga gwamnatin Saudiyya ta sake shi”.
 • Shirin Newsnight na BBC ya ce kasashen yammaci ba sa iya sukar gwamnatin Saudiyya kai tsaye saboda kwangilar makamai mai tsoka da Saudiyyar ke bayarwa.
 • Saudiyya ce ta hudu a duniya (alkaluman 2013) wajen kashe kudi a fannin soji.
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane sun yi zanga-zanga tare da barkwanci kan bulalar