shekara ta 2014, ta fi kowacce dumi

Dumamar yanayi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dumamar yanayi

Shekarar 2014 an ce ita ce ta fi kowacce shekara dumi a tarihi saboda yanayin dumamar duniya ya kai mataki na 0.68C fiye da kiyasin da aka yi na wasu shekaru - wannan sakamako ne na binciken da masana kimiyya a Amurka suka gudanar.

Sakamakon ya nuna cewar an samu shekaru 14 cikin 15 masu dumi a tarihi tun lokacin da aka shiga wani sabon karni.

Masu bincike ne na hukumar kula da binciken sararin samaniya ta Amurkar Nasa da Noaaa suka buga sakamakon binciken a ranar Jumma'a.

A watan da ya gabata, hukumar kula da binciken yanayi ta duniya ta bayar da wasu alkaluman share-fage da suka yi hasashen da ya nuna cewar watanni 12 za su zamo watanni masu dumi da ya zarce duk wani dumin da aka taba ji.

An yi hasashen yanayin ne na dogon zango daga wasu bayanai da aka tattara tun daga shekara ta 1951 da kuma shekara ta 1980.

Gadvin Schmidt daraktan Cibiyar nazarin binciken sararin samaniya ta Goddard ya ce wannan ita ce ta baya-bayan nan a jerin shekaru masu dumi.

Ya kara da cewar "a yayinda aka dora kowacce shekara a kan ma'aunin bincike na yanayin da kowacce shekarar ta kasance, a dogon zango ana danganta shekarun ne da sauyin yanayi da a yanzu ake samu sakamakon hayakin da mutane ke fitarwa."

Hukumomin Nasa da Noaa na Amurka sun yi aiki da bayanan yanayin dumamar diuniya na biyu cikin ukku na binciken da aka gudanar, amma hukumar binciken yanayi ta Brittaniya ta yi aiki ne da bayanan binciken na ukku.

Hukumar binciken yanayi ta duniya tana amfani ne da bayanai daga dukkansu ukku, kuma wannan ne ta yi amfani da shi wajen bayar da alkaluman da ta bayar na yanayi a duniya a cikin watan Disamba.

Lokacinda yake magana da 'yan jarida, Dr Schmidt ya ce sakamako daga wadannan bayanan biyu sun nuna akwai dumi sosai a tekunan duniya.

Karin bayani