Mutane biyar aka kashe a sabon harin Gombe.

Mutanen da suka mutu a harin Gombe
Image caption Mutanen da suka mutu a harin Gombe

Mutane akalla biyar ne suka rasa rayukansu wasu kimanin goma suka jikkata a birnin Gombe, sakamakon wani sabon harin bam na kunar bakin-wake da aka kai jiya da misalin karfe bakwai da minti goma sha biyar na yammaci.

An kai harin ne a wata kwarya-kwaryar kasuwa dake Unguwar Arawa a cikin birnin, kuma shi ma dan kunar bakin-waken ya mutu, inda gawarsa ta yi kaca-kaca sanadiyar tashin bam din.

Wannan hari da jami'in hudda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar ya tabbatar, ya nuna cewa dan kunar bakin-wake ne.

Jami'an tsaron sun yi kira ga mutane su kara sa ido, domin alhakin tabbatar da tsaro, ba wai kawai gare su ya rataya ba, har da su kansu al'ummar kasa.

Karin bayani