Zanga-zanga ta kara barkewa a Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption zanga-zanga a jamhuriyar Niger

Rahotanni daga jamhuriyar Niger na nuna cewa dubban matasa ne suka yi dandazo a babban masallacin da ke babban birnin kasar,Niamey, a yau Asabar, don nuna kin jinin hoton batanci da jaridar kasar Faransa,Charlie Hebdo, ta yi ga Manzon Allah.

Kimanin matasa 1,000 ne dai suka fito zanga-zangar, a inda wasunsu suke kiran 'Allahu Akbar',wasu kuma suna kona tayoyi sannan suna jefa duwatsu ga 'yan sandan dake sanya musu hayaki- mai-sa-kwalla.

Yanzu haka an ce matasa sun fito suna ta kona coci-coci da gidajen giya da na caca. Kawo yanzu dai mace daya ce ta rasa ranta sakamakon zanga-zangar.

Ko a ranar Juma'a ma dubban matasa a kasar ta Niger sun gabatar da irin wannan zanga-zangar a birnin Zinder, al'amarin da ya yi sanadiyar mutuwar dan sanda daya da mutane uku, sannan mutane 45 suka jikkata.

An kona coci guda uku da kuma cibiyar raya al'adun kasar Faransa sakamakon zanga-zangar ranar Juma'a.