Kura ta lafa a Nijar bayan zanga-zanga

Zanga-zanaga Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto
Image caption Zanga-zanaga Jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar kura ta lafa bayan zanga-zangar kin jinin batanci da mujallar Faransa wato Charlie Hebdo ta yi wa Manzon Allah.

Zangar-zangar ta fara ne a bayan sallar Juma'a a birnin Damagaram, kana a ranar Asabar ta bazu zuwa biranen Maradi da Yamai. babban birnin kasar, inda aka ce an kona coci-coci guda bakwai da wasu kadarorin kasar Faransa.

Ko da yake ba a samu rahoton asarar rayuka ba kamar yadda aka samu a ranar Jumma'a. A ranar Jumma'ar an ce tashin hankalin ya yi sanadiyar mutuwar biyar, yayin da wasu kamar 45 suka samu raunuka.

Fira ministan kasar, Biriji Rafini, ya gana da Shugabannin addininan Musulunci da na Kirista a kasar, inda ya bayyana takaicinsa game da faruwar lamarin.

Ya ce tabbas babu dadi a muzanta kowane addini, amma ba dalili ba ne da zai sa wasu bata gari su aikata abin da suka aikata.

Ya kuma yi kira ga duka bangarorin da su sansanta tare da yafe wa juna tare da yi wa mabiyansu tarbiyya don wanzuwar zaman lafiya.