Ina da cikakkiyar lafiya- Buhari

Janal Muhammadu Buhari. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janal Buhari yace jita-jita ce kawai ake yadawa, dan a daukewa 'yan Najeriya hankali kan matsalolin da jam'iyyar PDP mai mulki ta sanya su ciki.

A Najeriya, dan takarar shugaban kasar a inuwar babbar jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari ya ce labarin da ake yadawa cewa ba shi da cikkakar lafiya karya ce tsagawaronta.

A wajen wani taron manema labarai a Abuja a jiya Lahadi, Janar Buhari ya ce wadanda ke yada wadannan labaran sojojin haya ne da aka dauko domin su kauda hankalin 'yan kasar daga halin da jam'iyya mai mulki ta PDP ta jefa su.

''To ni dai lafiya ta kalau, idan sun san likitoci na su je su tabbatar da hakan, siyasa ce kawai ana biya domin a watsa labarai, an kashe arzikin kasa, babu tsaro gwamnatoci ba sa iya biyan albashi dan haka ana son kauda hankalin mutane daga kan abinda ya dame su'', inji Buhari.

A ranar jumu'a ne gwamnan jihar Ekiti na Jam'iyyar PDP Ayo Fayose ya fitar wata sanarwa yana cewa ya kamata 'yan Najeriya su binciki lafiyar jagoran na 'yan adawa.