Babu sauran mai dauke da cutar Ebola a Mali

Shugaba Boubacar Keita Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata yarinya ce ta fara shigowa kasar Mali da cutar Ebola daga makwafciyar kasar Guinea.

Gwamnatin kasar Mali ta ayyana kasar a matsayin wadda ba ta dauke da ko mutum guda mai cutar Ebola.

Ministan lafiyar kasar Ousmane Kone shi ne ya bayyana haka ya yin taron manema labarai.

Inda yace bayan shafe kwanaki 42 ana sanya idanu, ba a samu wani da aka ce ya na dauke da kwayar cutar Ebola ba kamar yadda shugabannin lafiya na kasashen duniya suka sanar.

A yau 18 watan junairu kasar Mali na daga cikin jerin kasashen da ta kakkabe kwayar cutar Ebola daga cikinta.

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar Ebola a kasar Mali, wadda ta kasance daya daga cikin kassahe shida na yammacin Afurka da cutar ta bulla.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kawo yanzu cutar Ebola ta hallaka fiye da mutane 8000, yawancinsu a kasashen Guinea, da Liberia, da kuma Saliyo.