Ba mu goyon bayan batanci ga Islama

Zanga-zanga a Nijer Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanga-zanga a Nijer

Mabiya addinin Kirista a Jumhuriyar Nijer, sun koka da bannar da aka yi musu, suna cewar ba mu goyon bayan batanci ga duk wani addini.

Pasto Sani Nomao, wakili a kwamitin Inganta danganta tsakanin addinai a jamhuriyar Niger, ya ce sun yafe abinda ya faru yayin zanga-zangar da mabiya addini musulunci suka yi a cikin kasar.

Pastor Sani Nomao ya shiadawa wakiliyar mu ta Maradi cewa sam ba su goyon bayan batancin da jaridar nan ta barkwanci ta kasar Farasansa Charlie Hebdo ta yi ga Annabi Muhammad SAW.

Pastor Nomao ya kara da cewar ko da mutum ba addinin musulunci, ko na kirasta yake yi ba, sam ba za su goyi bayan a ci zarafin abinda ya yi imani da shi ba.

Ya yi kira ga musulmi da kirista a jamhuriyar Niger da su yafewa juna, su ci gaba da zaman lafiya tsakaninsu.

Karin bayani