An rage kudin man fetur a Nigeria

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Faduwar farashin danyan mai a kasuwannin duniya, na daga cikin dalilan da suka sanya farshin man fetur ya yi kasa.

Ministar man fetur a Nigeria Mrs Diezani Alison-Madueke ta sanar da cewar an rage kudin man fetur a kasar.

An rage kudin man ne daga naira 97 zuwa naira 87 kowacce lita daya, kuma wannan farashi zai fara aiki ne daga karfe 12 daren ranar lahadin nan 18 ga watan Junairu 2015.

Sanarwar ta umarci sashen kula da albarkatun mai da kuma kayyade farashin man fetur wato PPRA, ya tabbatar da an bi umarnin.