An kai harin bam a Potiskum

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Yobe na daya daga cikin jihohi uku da suka fi fama da hare-haren Boko Haram a Najeriya

Akalla mutane biyar ne suka mutu da dama suka jikkata a wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai a mota a Potiskum ta jihar Yobe a Najeriya.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a wata tashar mota da ke kusa da wani gidan mai, a kan titin Jos Road, da safiyar Lahadi.

Wani wanda ya ga lamarin ya gaya wa BBC cewa bom din ya fashe ne yayin da wani mutum ya zo a cikin karamar mota kirar Golf, ya kuma tsaya kamar zai dauki fasinjoji.

Rahotanni sun ce harin ya rutsa da wata yarinya, da dan kunar-bakin-waken ya kirawo domin ya sayi ruwa a wurinta.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki nauyin kai harin, wanda ya yi kama da ire-iren wadanda ake dangantawa da kungiyar Boko Haram.