2015: Ina da koshin lafiya - Janar Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari ya ce gwamnati ba ta yi wa 'yan Najeriya komai ba shi ya sa take yada miyagun labarai a kansa.

A Najeriya, dan takarar shugabancin karkashin jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari, ya ce labarin da ake yadawa cewa ba shi da cikakkiyar lafiya karya ne.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Lahadi, Janar Buhari ya ce wadanda ke yada wadannan labaran sojojin haya ne da aka dauko domin su kawar da hankalin 'yan kasar daga halin da jam'iyya mai mulki ta PDP ta jefa su.

Ya ce, ''To ni dai lafiya ta kalau, idan sun san likitoci na su je su tabbatar da hakan, siyasa ce kawai; ana biya domin a watsa labarai, an kashe arzikin kasa, babu tsaro, gwamnatoci ba sa iya biyan albashi don haka ana son kawar da hankalin mutane daga kan abin da ya dame su''.

Janar Buhari ya kara da cewa wannan batu ba zai kawar da hankalin 'yan Najeriya daga zabensa ba.

A ranar Juma'a ne gwamnan jihar Ekiti na Jam'iyyar PDP Ayo Fayose ya fitar wata sanarwa yana cewa ya kamata 'yan Najeriya su binciki lafiyar jagoran na 'yan adawa.