Ana ci gaba da sayar da fetur a kan N97

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu gidajen mai na 'yan kasuwa suna kukan sun sayi man da tsada

A Najeriya, duk da umarnin da gwamnati kasar ta bayar na rage farashin man fetur daga N97 zuwa N87, har yanzu masu gidajen mai na 'yan kasuwa na ci gaba da sayar da man kan tsohon farashi.

Wasu masu gidajen man suka ce ba za su fara sayar da man a kan sabon farashin ba sai sun sayar da wanda suka riga suka sayo a tsohon farashi.

Mista Chukudi Ezenwa na kungiyar IPMAN a kasar ya ce ya kamata gwamnati ta ba su lokaci domin ganin ba su yi asara ba.

Wasu jama'ar kasar sun koka da yadda masu gidajen man na 'yan kasuwa ba su fara sayar da man a sabon farashin ba.

Ci gaba da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ya sa gwamnatin Najeriya ta rage farashin man a cikin kasar, kodayake wasu na ganin an yi hakan ne domin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan.