Amurka ta saci bayanan Korea a 2010 - Rahoto

US Hakkin mallakar hoto .
Image caption Korea ta Arewa na ci gaba da musanta zargin kutsen

Wani rahoto ya nuna cewa Amurka ta yi kutse a kwamfutocin kasar Korea ta Arewa a shekarar 2010.

Rahoton wanda jaridar New York Times ta wallafa ya kara da cewa hakan ya sa Korean ta yi kutse a kamfanin Sony na kasar ta Amurka.

Jaridar ta kafa hujjar rahoton ta ne akan wasu takardu da samu ta samu ta bayan fage na hukumar tsaron kasar ta Amurka.

New York Times ta kara da cewa wasu na'urori da aka dasa ne suka bayyanawa hukumar tsaro ta fararen kaya cewa Korea na kutse a kamfanin Sony.

Korean dai ta musanta wannan zargi da Amurkan ke mata.

Masu bincike a Amurka sun ce Korea ta Arewan ta shafe watanni biyu ta na hada wani jadawali na kamfanin Sony kafin ta fara yin kutsen a cewar jaridar.

Wannan kutse da aka yi a kamfanin na Sony ya fitar da wasu bayanai da suka nuna irin kudaden da ake biyan manyan ma'aikatan kamfanin.

Kutsen har ila yau ya sa an dage fitar da wani wasan barkwanci da kamfanin ya shirya wanda ke nuna yadda aka kashe shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong-un.

Koda ya ke daga baya an fitar da fim din a kafar intanet.