Rundunar soji ta ɓara kan takardun Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janar Buhari tsohon shugaban mulkin soji a Nigeria ne

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi karin haske a kan takaddamar da ake ta yi dangane da takardun shaidar karatun sakandare na dan takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jam'iyya adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

Daraktan yada labarai na rundunar Birgediya Janar Olajide Laleye, ya gabatar da wasu takardu da ya ce su ne a fayil din tsohon shugaban kasar na mulkin soja.

Batun takardun shaidar kammala karatun sakandare na Janar Buhari dai na cikin batutuwa da ke jawo cece-kuce musamman a kafofin yada labarai, kasa da wata guda a gudanar da babban zaben kasar.

Birgediya Janar Laleye ya ce rundunar ta yanke shawarar yin wannan bayani ne sakamakon bukatun da mutane da dama suka mika mata na bayani dangane da batun.

Ya ce "Takardun da muke da su sun nuna cewa Manjo Janar Muhammadu Buhari ya aike da takardar neman shiga aikin soja ne lokacin yana aji shida na makarantar sakandaren lardi ta Katsina ranar 18 ga watan Oktoba, 1961."

"Bisa al'ada kafin mutum ya zama jami'i a rundunar sojin kasa ta Najeriya, sai wata hukumar tantancewa ta tabbatar da ingancin takardun shaidarsa na asali. Sai dai kuma babu wani bayani da ke nuni da cewa a kan yi hakan a shekarun 1960," in ji Laleye.

Lalaye ya kara da cewa "Amma fa babu takardar shaidar ta asali ko kwafenta ko ma takardar sakamakon jarrabawar Janar Muhammadu Buhari a fayil dinsa."