Tattalin arzikin China ya samu koma-baya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnati ta ce za a fuskanci matsi a kasar

Tattalin arzikin China ya samu koma-bayan da bai taba fuskanta ba a cikin shekaru 20 da suka wuce.

Alkaluman tattalin arziki sun nuna cewa tattali arzkin kasar ya fadi da kaso bakwai da digo hudu a shekarar 2014.

Wannan shi ne karon farko a cikin shekaru goma da tattalin arzikin China ya gaza kai wa hasashen da kasar ta yi.

Gwamnatin kasar dai tana gagargin 'yan kasar su tsammaci tafiyar-hawainiya a farfadowar tattalin arziki, sannan su shirya wa fuskantar tsare-tsare da za su kuntata musu.