Musulmai ne suka fi mutuwa a hare-haren ta'addanci?

Duniya ta san irin ayyukan rashin imanin da masu da'awar kishin Islama ke aikatawa sakamakon irin hare-haren da suke kai wa kamar wanda aka kai a kan mujallar Charlie Hebdo.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty

Sai dai bayan harin na Paris wani malamin addinin Musulunci ya shaida wa BBC cewa Musulmai ne mafi yawan wadanda hare-haren ta'addanci ya fi shafa a fadin duniya.

To ko ya gaskiyar hakan? Wani shiri na BBC ya yi kokarin bincike kan hakan. Bayan kisan da aka yi a Charlie Hebdo, Hassen Chalghoumi wani malamin addinin Musulunci da ke Paris ya shaida wa BBC cewa kashi 95 cikin dari na wadanda hare-haren ta'addanci ya fi shafa a fadin duniya Musulmai ne. A yammacin duniya mutane za su ji mamakin hakan, domin da anyi maganar ta'addanci abin da ke zo musu a rai su ne hare-hare kamar na Charlie Hebdo, da wanda aka kai a tashar jirgin kasa na London da kan motoci kirar bas da harin da aka kai kan jirgin kasa a Madrid sai kuma harin ranar 11 ga watan Satumba da aka kai Amurka.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Hakkin mallakar hoto AFP Getty

Irin wadannan hare-haren an kaisu ne domin aja hankali kuma an cimma hakan. Kuma duk da cewa Musulmai na cikin wadanda suka rasa rayukansu a wadannan hare-hare, mafi yawa ba Musulmai ba ne. Saboda haka menane gaskiyar kashi 95 cikin dari da aka fada? Wani shirin BBC ya duba kididdigar. Shirin ya gano cewa kashi 95 cikin darin ya samo asali ne daga wani rahoto na cibiyar yaki da ta'addanci na gwamnatin Amurka, wanda aka wallafa a shekarar 2011. Kuma ga abin da rahoton ke cewa "A inda ake iya gane addinin wadanda hare-hare suka shafa, Musulmai ne kashi 82 zuwa 97 cikin dari na wadanda suka mutu a cikin shekaru biyar da suka wuce." Saboda haka wadannan alkaluma sun jaddada abin da malamin ya fada. Sai dai akwai wata togaciya a rahoton wato "Inda ake iya gane addinin wadanda harin ta'addancin ya shafa." To domin gano tartibin abu game da wadanda harin ta'addanci ke shafa a duniya, akwai bukatar mu san cewa ko a mafi yawan lokuta ne ake gane addinin wadanda hare-haren ya rutsa da su ko kuwa a wasu lokuta kalilan ne kawai. Wata tawagar masana kan aikata manyan laifuka da masana a fannin kididdiga da ke jami'ar Maryland sun kwashe shekaru 40 suna tattara bayanai kan ta'addanci a duniya a cikin wani kundi, kuma daga wannan kundin ne Amurka ke samun alkalumanta. Masanan na duba rahotannin kafafen yada labarai don tantance hare-haren da aka kai. Akwai wasu hanyoyin da masanan ke bi wajen tantance wannene harin ta'addanci wadanda suka hada da sai hari ya shafi kasashen duniya, kuma an zubar da jini ko mai barazana haka kuma sai wadanda ba gwamnati ba ce ta kai su. Sannan kuma suna duba cewa ko hari na da alaka da siyasa da tattalin arziki ko kuma don cimma wata manufa ta addini, kana domin aike wa da wani sako ga mutane da dama ba wai kawai wadanda harin ya shafa ba. Haka kuma suna hada wa da duk wani tashin hankalin da ba ya cikin sigar yakin da aka amince da shi a hukumance. Sai dai abin lura a nan shi ne masanan na jami'ar Maryland sun dogara ne kan rahotannin kafafen yada labarai, kuma a mafi yawancin lokuta ba sa dauke da bayanai kan addinin wadanda abin ya shafa. Amma akwai wasu bayanai wadanda suka shafi yankuna na duniya maimakon addini. A cikin shekaru goma da suka gabata daga shekarar 2004 zuwa 2013, kusan kashi 50 cikin dari na dukkanin hare-hare da kuma kashi 60 cikin dari na mutuwar da ake samu a hare-haren ta'addanci suna faruwa ne a kasashe uku - Iraq da Afghanistan da kuma Pakistan. "Mafi yawan al'ummar wadannan kasashe dai Musulmai ne, haka kuma mun san cewa kashi 80 zuwa 90 cikin dari na hare-haren da ake kai wa sun shafi cikin gida ne maimakon kasashen ketare" In ji shugaban tawagar masanan jami'ar Maryland Erin Miller. Saboda haka wadanda suka mutu ko jikkata a hare-haren sun fi zama fararen hula, domin tun da wuraren da suka fi fuskantar harin ta'addancin mafi yawan kasashen Musulmai ne kuma maharan ma Musulmai ne to suma wadanda abin ke rutsawa da su za su kasance Musulmai. Idan aka yi la'akari da alkaluman da ake da su a cikin shekaru goman da suka wuce daga shekarar 2004 Burtaniya ta fuskanci hare-haren ta'addanci 400 kuma yawancinsu a Ireland ta arewa ne kuma mafi yawa daga cikinsu ba su kai ga asarar rayuka ba. Amurka ita kanta ta fuskanci hare-hare 131 kuma kasa da 20 ne a cikinsu suka kai ga mutuwa, yayin da Faransa ta fuskanci hare-hare 47. Amma a kasar Iraqi an samu hare-hare 12,000 kuma 8,000 daga cikinsu an rasa rayuka. Erin Miller ya lissafa cewa, idan aka yi la'akari da wadannan bayanai kididdigar da aka bayar na kashi 95 cikin dari ta dan yi yawa, amma kuma tana kan hanya.