Buhari: Birnin Kano ya cika ya batse

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Talakawa na son Janar Buhari

'Yan takarar shugabancin Nigeria na manyan jam'iyyun kasar suna ci gaba da yakin neman zabe a fadin kasar domin zawarcin masu kada kuri'a.

Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar adawa ta APC zai je birnin Kano a ranar Talata inda yake da miliyoyin magoya baya.

Wakilin BBC a Kano ya ce filin wasa na Sani Abacha ya cika makil da dubun dubatan mutane tun kafin isowar Janar Buhari.

A ranar Laraba ne ake saran Shugaba Goodluck Jonathan zai je Kano domin yakin neman zabe.

A ranar 14 ga watan Fabarairu ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria wanda masu sharhi suka ce zai yi zafi fiye da duk zabukan da aka yi a baya.