An kammala taro kan tsaro a Nijar

sojojin Kamaru

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Sojojin Kamaru

A Jamhuriyar Nijar an kammala wani taron kasa-da-kasa, wanda kasashen yankin tafkin Cadi suka shirya domin yaki da boko haram.

Ministan harkokin wajen Nijar , Malam Bazoum Muhammad ya ce taron ya cinma wasu abubuwa muhimmai guda biyu.

Na farko ya bukaci kungiyar Tarayyar Afurka(AU) ta gabatar wa majalisar dinkin duniya wani kuduri da zai taimaka wajen samar da kudade da kayan aikin da ake bukata don cimma wannan manufa.

Haka nan ya ce sun amince su sauya hedkwatar rundunar dakarun hadin gwiwa daga Baga, a jihar Borno ta Nijeriya, inda Boko Haram ta kwace, zuwa birnin Ndjamena na kasar Chadi.