Amurka za ta bude sabon babi - Obama

US Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Lokaci ya yi da Amurka za ta daina shiga yake-yake

Shugaban Amurka Barrack Obama ya ce lokaci ya yi da kasar za ta rufe babin tsunduma kanta a cikin yake-yake, da koma-bayan tattalin arziki da aka fuskanta na wasu tsawon shekaru.

A jawabin da ya gabatar game da halin da kasar ke ciki, Shugaba Obama ya ce tattalin arzikin kasar ya na habaka cikin sauri tun daga shekarar 1999, tare da samar da guraben ayyukan yi.

Ya kuma kara da cewa ce zai yi amfani da karfin ikonsa wajen hana ko wane kudurin doka da ke barazanar dakushe nasarorin da gwamnatinsa ta samu a kan tsare-tsaren inshorar lafiya, da tsarin karbar baki, da kuma hada hadar kudade.

"Ba za mu iya cire kariyar da iyalai ke da ita ba ta inshorar lafiya, sannan ba za mu koma baya muna tunkarar batun tsarin karbar baki da muka riga muka wuce wurin baya ba." Obama ya ce.