2015: "PDP na fuskantar matsi"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu sharhi sun ce PDP na fuskantar matsi shi ya sa suke cewa Buhari zai mutu

Wasu masu sharhi a Najeriya sun ce matsin da jam'iyyar PDP mai mulki ke fuskanta na yiwuwar rasa mulki ne ya sa take fatan dan takarar jam'iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya mutu.

A ranar Litinin ne dai wasu jaridun kasar suka wallafa wani talla da gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya ba su, inda yake cewa bai kamata a zabi Janar Buhari ba domin kuwa zai iya mutuwa kan mulki kamar yadda wasu shugabanni daga arewacin kasar kamar Janar Sani Abacha da Umaru Musa 'Yar adua suka yi.

Sai dai a hirar da BBC ta yi da wani mai sharhi, malam Mannir Dan Ali ya ce "[PDP] su na jin cewa kamar al'amura na neman subuce musu shi ya sa suke yin talla irin wannan. Duk irin wannan kokari ne wajen ganin sun kawo shakku ga masu zabe domin kada su zabe shi".

Ya kara da cewa jam'iyyar ta PDP za ta ci gaba da yin irin wadannan miyagun fata har sai lokacin zabe ya yi.

Wannan batu dai ya bata wa 'yan kasar da dama rai, suna masu cewa abin takaici ne PDP ta rika yin fatan ganin Janar Buhari ya mutu.

A makon jiya ma dai sai da Janar Buhari ya musanta zargin da ake yi cewa ba shi da cikakkiyar lafiyar jagorantar kasar, yana mai cewa lafiyarsa lau.