Ana zaben shugaban kasa a Zambia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Micheal Sata ya mutu ne a wani asibiti da ke London

Ana gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Zambia, bayan mutuwar Shugaba Michael Sata a watan Octoban shekarar da ta wuce.

Wakiliyar BBC a Lusaka babban birnin kasar ta ce ana tafka ruwan sama tun da sanyin safiya, amma mutane sun fito da lemominsu, suna kokarin tabbatar da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na zabar wanda suke so.

Edgar Lungu na jam'iyyar da ke jan ragamar mulki yana fuskantar Hakainde Hichilema ne na jam'iyyar adawa ta United Party for National Development.

Dukkanin 'yan takarar sun yi alkawarin kyautata tsarin ilimi na kasar da kuma samar da guraben aiki.