An yi sauyi a shafin intanet din BBC

BBC
Image caption Tsarin zai kara kusantar da masu ziyartar shafin BBC

An samu gagarumin sauyi a shafin intanet na BBC domin karfafa dangantaka da masu ziyarar shafin.

Yanzu masu ziyartar shafukan za su iya kara wasu tsare-tsare a saman shafin na BBC da suke bukata.

Misali, baya ga sashen labaran Burtaniya da na siyasa masu ziyartar shafin za su iya kara wani abu daban da suke bukata.

Wannan sauyi wani yunkuri ne na yin garanbawul ga fuskar shafin na BBC.

Tuni dai wasu masana ke gargadin cewa wannan sauyi zai iya haifar da matsala ga masu shiga shafukan.

Amma a cewar shugaban BBC, sauyin zai inganta yadda masu shiga shafin ke neman bayanai.

"Mun san cewa muna da masu ziyartar shafin da dama, kuma mun lura suna nuna kauna ga shafin." In ji Robin Pembrooke.

Wannan sauyi wani yunkuri ne na kara kusantar masu shiga shafin in ji kamfanin na BBC.