2015: Jonathan ya yi gangami a Kano

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jonathan yana gangamin ne kwana guda bayan abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Buhari ya yi nasa a jihar

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi gangami a jihar Kano, a ci gaba da yakin neman zaben da yake yi.

Mr Jonathan ya isa Kano ne da safiyar ranar Laraba, inda 'yan jam'iyyarsa ta PDP suka tare shi.

Ana yi gangamin ne a filin wasa na Polo, kuma shugaban kasar ya sha alwashin bunkasa al'amura a Najeriya.

A ranar Talata ne dai abokin hamayyarsa na jam'iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya yi nasa gangamin a jihar ta Kano.