Murar tsuntsaye ta bulla a jihohi 7 a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana bukatar masu lura da kaji su yi hattara

Hukumomi a Nigeria sun tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye a jihohi bakwai na kasar.

Ministan ayyukan gona, Dr. Akinwumi Adesina ne ya sanar da bullar cutar kuma ya ce tuni har ta hallaka dubban kaji a fadin kasar.

Kwayar cutar ta H5N1 wacce ka iya yaduwa tsakanin tsuntsaye da bil adama ta bulla a jihohin Lagos da Kano da Rivers da Plateau da Ogun da Delta da kuma Edo.

A cewar ministan duk da bullar cutar amma kawo yanzu ba ta kai matakin annoba ba.

An ambato Dr Adesina yana cewa kaji fiye da dubu 140 ne suka harbu da cutar murar tsuntsaye kuma tuni cutar ta hallaka kaji fiye da dubu 22.

Ministan ya ce babu matsala mutum ya ci kwoi amma ana bukatar a dafa kaji da kyau kafin a ci.