Buhari ya gama sakandare a 1961- Kwaleji

buhari

Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Batun dai ya jawo cece-kuce a kasar ta Nigeria.

Kwalejin gwamnati a Katsina da ke Nigeria ta fitar da takardar shaidar kammala karatun sakandare na dan takarar shugabancin Nigeria a jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari.

Takardar ta nuna cewa ya kamalla karantun sakandare ne a shekarar 1961.

Janar Buhari ya samu sakamakon matakin 'credit' a darussan Ingilishi, da ilimin kasa, da Tarihi, da Kiwon Lafiya, da Hausa, ya kuma samu 'pass' a adabin Ingilishi, kamar yadda takardar ta nuna.

Jaridar Premium Times a Nigeria ita ce ta wallafa shaidar jarrabawar kammala sakandare na Janar Buhari din a ranar Laraba.

Batun takardun shaidar kammala karatun sakandare na Janar Buhari dai na cikin batutuwa da ke jawo cece-kuce musamman a kafofin yada labarai, yayin da ya ake kasa da wata guda a gudanar da babban zaben kasar.