Ghana na yin bincike kan kutse a intanet

Image caption Gwamnatin ta ce ta kwato ikon shafukan intanet din daga hannun wadanda suka yi kutsen

Gwamnatin Ghana ta kaddamar da bincike bayan 'yan damfara sun yi kutse a shafukanta na intanet ranar Laraba.

'Yan damfarar sun yi kutse ne a shafin intanet na gidan gwamnatin kasar mai suna (ghana.gov.gh) da na ma'aikatun sadarwa, da kananan hukumomi da masana'antu da harkokin kasashen waje.

Sai dai mataimakin ministan sadarwa, Ato Sarpong, ya ce "Ina da kwarin gwiwar cewa mutanen da suke mana aiki za su taimaka wajen gudanar da bincike kan wannan batu, sannan mu samu damar kare manhajojinmu na intanet da zummar kare aukuwar haka".

Sarpong ya kara da cewa gwamnati ta sake kwato ikon shafukan daga mutanen da suka yi kutsen.