John Kerry ya yi kirarin nasara a kan Isis

John Kerry Hakkin mallakar hoto AFP

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce yana jin an kashe kusan rabin shugabannin kungiyar I S daga lokacin da kasashen duniya suka fara kai musu farmaki zuwa yau.

Ya kuma ce an kwato yanki mai fadin murabba'in kilomita dubu goma sha takwas daga hannun dakarun na I.S.

Faraministan Iraki, Haider Al'abadi, wanda shi ma ya halarci taron, ya ce ya samu tabbacin cewa za a ci gaba da tura wa kasarsa da makamai, duk da matsalar karamcin kudin da take fuskanta sakamakon faduwar farashin danyen mai.

Da yake zantawa da BBC gabanin soma taron, Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya, Philiph Hammond, ya yaba wa kokarin da gwamnatin Iraki ke yi na tabbatar da rundunar sojanta suna aiki yadda ya kamata, amma ya jaddada cewa har yanzu da sauran shiri ga sojojin kafin su kai karfin tunkarar IS:

Ya ce, "Sabuwar gwamnatin Iraki ta yi ta-maza da sallamar wani adadi mai yawa na manyan jami'an sojoji da ake jin ba su tabuka komai ba.

"Do haka muna sake yi wa rundunonin sojin Iraki garambawul , tare da sake ba su horo da kuma makamai.

Amma dai za a yi watanni kafin a ce sun shirya ma shiga yaki gadan-gadan.''