Boko Haram: Nigeria na shirin sauya kundin tsaro

Nigeria Hakkin mallakar hoto .
Image caption Lokaci ya yi na sauya kundin tsaron Najeriya - Masana

A Najeriya, wani kwamiti na jin ra'ayoyin jama'a domin duba yadda za a sauya kundin tsaron kasar.

Kwamiti yana zaga wa wasu sassa na kasar ne domin jama'a su ba da ta su gudunmuwa a wannan fanni.

Sababbin kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta, kamar yadda masu sharhi suka nuna, na cikin batutuwan da suka sa ala tilas ake shirin sauya manufofin tsaron kasar.

Najeriya ta kwashe sama da shekaru biyar tana fama da matsalar hare-hare, wadanda ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa a arewa maso gabashin kasar.

Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar dubban mutane yayin da sama da mutane miliyan daya suka fice daga gidajensu domin tserewa rikicin.

Masana harkar tsaro a Najeriyar sun ce lokaci ya yi da kasar za ta duba kundin idan aka yi la'akari da cewa an dade ba a yi hakan ba.