Cutar Ebola ta ragu a kasar Liberia

Shugabar kasar Liberia Hellen Johnson Sirleaf
Image caption Cutar Ebola ta hallaka kusan mutane dubu tara a kasar liberia kadai.

Mataimakin ministan lafiyar kasar Tolbert Nyenswah, ya ce hakan na nufin nan ba da jimawa ba kasar za ta kakkabe cutar baki daya.

Sai dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewar kada ai saurin yin sakaci, ta yiwu cutar Ebolar na yaduwa a yankunan da jami'an lafiya ba su da masaniya akai, kuma har yanzu ana cikin hadarin yaduwar Cutar.

Akalla mutane kusan dubu tara cutar Ebola ta hallaka a kasar Laberia kadai, ya yin da kasashen Guinea da kuma Saliyo suke kokarin kakkabe ta saboda agajin da aka samu daga kasashen waje.