Nigeria: Shafin intanet na soji ya koma aiki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Olukolade ya ce an yi kutsen ne yadda ISIS ke yin kutse

Rundunar sojin Najeriya ta ce shafinta na intanet ya koma aiki bayan masu kutse a shafukan intanet sun yi kutse a cikinsa.

Kakakin shelkwatar tsaron kasar, Manjo Janar Chris Olukolade ya ce kamfanin da ke kula da shafin nasu ne ya yi aiki domin dawo da shafin.

Ya ce an yi kutsen ne irin yadda kungiyar da ke ikirarin kishin Islama, ISIS ke yi.

Bai yi karin bayani kan abin da yake nufi ba.

A kwanakin baya ma dai kakakin shugaban kasar, Reuben Abati ya ce masu kutse sun yi amfani da adireshinsa na email wajen aike wa da sakonni zuwa ga manema labarai.