Sarki Salman ne ya gaji Sarki Abdullah

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sarki Salman ne ke jagorancin kasar lokacin da aka kwantar da Sarki Abdullah a asibiti

Sarki Abdullah Bin Abdulaziz na Saudi Arabia ya rasu yana da shekaru casa'in a duniya.

Ya kwashe makonni da dama ana fama da cutar namoniya a asibiti.

A ranar Juma'a ne za a yi jana'izarsa.

Dan uwansa Salman ne -- mai shekaru 79 -- ya gaje shi.

Sarki Abdullah ya hau karagar mulki a shekarar 2005.

Sarki Abdullah ya kawo sauye-sauye a kasar wadanda suka hada da yin garanbawul ga rundunar 'yan sanda da bai wa mata damar kada kuri'a a lokutan zabe.

Shugabannnin kasashen duniya sun fara jajen rasuwar Sarki Abdullah.

Sarki Abdullah II na Jordan ya katse taron da yake yi kan Tattalin arzikin duniya a birnin Davos na Switzerland domin tafiya Saudi Arabia wajen jana'iazar Sarki Abdullah.

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ne zai jagoranci tawagar kasar wajen jana'izar.

Shugaba Obama ya aike da ta'aziyyarsa ga Saudi Arabia.

Shi ma Firai Ministan Burtaniya David Cameron, da shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani sun mika tasu ta'aziyyar.