An yi jana'izar Sarki Abdullah a Riyadh

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi wa Abdullah Sallah ne a wani Masallaci a Riyadh

An yi jana'izar Sarki Abdullah na Saudi Arabia a birnin Riyadh bayan ya rasu a daren ranar Alhamis yana da shekaru 90.

Margayi Abdullah ya rasu ne bayan doguwar jinya sakamakon fama da cutar nimonia.

An birne Sarkin a wani kabari mara alama a birnin Riyadh.

Sarki Abdullah ya hau karagar mulki a shekarar 2005.

Sabon sarkin Saudi Arabia, Sarki Salman bn Adul-Azizi al Saud, ya ce zai ci gaba da aiki kan manufofin marigayi Sarki Abdalla wanda ya rasu ranar Alhamis.

A wani jawabi da ya gabatar a gidan talbijin na kasar, sabon sarkin ya yi kira ga kasashen Musulmi na Larabawa da su hada kai su kuma zama masu sadaukarwa.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service