Shirin samar da kwamfutar Windows 10

Microsoft Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Windows 10 za ta kunshi har da na'urar jin magana

Kamfanin Microsoft ya bayyana cewa shirin samar da kwamfutar Windows 10 za ta zo da wasu sauye sauye.

Daga cikin sauye sauyen akwai na'urar jin magana da za ta fito da shi ta tsarin yadda ake sarrafa ta inda zai dinga ba da hasashe kan al'amuran duniya.

A cewar kamfanin tsarin yadda ake sarrafa kwamfutar zai ba da damar samar da wasu manhajoji da ke akwai a Windows 8 da Windows 7 da sauran su.

Da yawa dai ana ganin wannan garabasa za ta sa mutane su karbi Windows 10 hanu bi-biyu.

Wani mai sharhi kan harkokin kwamfuta ya ce dama akwai bukatar kamfanin na Microsoft ya sauya wannan fannin.

"Mun san cewa kusan kashi 10 na kwamfutoci suna dauke ne da manhajar windows 8, kuma hakan ya banbanta a tsakanin kamfanoni." In ji Frank Gillet.

A nashi ganin ba kasafai masu kera kwamfutoci suke maida hankali kan nau'in Windows ba domin neman kasuwa.

Ya kara da cewa yanzu haka hankali ya fi karkata ne zuwa kananan wayoyi na hanu irinsu Ipad da Android.