An ki amincewa da murabus na shugaban Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zangar sun ki amincewa da murabus din da shugaban kasar ya yi

A kasar Yemen, dubun dubatar masu zanga-zanga ne suka tunkari gidan shugaban kasar mai murabus, Abdurrabu Mansur Hadi, don nuna rashin amincewarsu da murabus din da ya yi ranar Alhamis.

Masu zanga-zanga sun nuna adawarsu ga 'yan tawayen Husawa, mabiya akidar Shi'a, wadanda suka kame birnin San'a.

Sun bukaci ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki, duk kuwa da matsin-lambar da 'yan tawayen kasar ke yi.

Masu zanga-zangar suna furta wasu kalamai da ke sukar Husawa.