'Yan Boko Haram suna kai hari a Maiduguri

Mayakan Boko Haram Hakkin mallakar hoto .
Image caption Mayakan Boko Haram

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya sun ce wasu mahara da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari da safiyar lahadi a birnin, a wani yunkuri na shiga don mamaye birnin.

Rahotannin sun nuna cewar maharan suna cigaba da fafatawa da sojoji dake kokarin hana su shiga birnin.

Babu dai wani cikakken bayani game da lamarin, amma rahotonnin sun ce, Jama'a a birnin sun afka cikin wani mummunan hali na rudani, yayinda kowa ke kokarin ceton ransa.

A birnin na Maiduguri ne daruruwan dubban mutanen da 'yan Boko Haram din suka kwace Kauyuka da garuruwansu suke zaman gudun hijira.

Harin na baya-bayan nan dai na zuwa ne kasa da sa'oi ashirin da hudu da rangadin yakin neman zabe da Shugaba Goodluck Jonathan ya kai a birnin, inda ya shaida ma 'yan jihar ta Borno da mutanen yankin arewa maso gabashin kasar cewa, nan ba da jimawa ba, gwamnatinsa za ta dauki matakai na kawo karshen hare-haren.

Karin bayani