An hana fita a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ko a watan Disamban shekara ta 2013 dai mayakan sun yi yunkurin kama birnin na Maiduguri.

A Najeriya, an kafa dokar hana-fita a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, bayan wani hari da 'yan kungiyar boko haram suka kai, wanda ake jin cewa ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Jami'an sojin Najeriya dai sun ce sun kaddamar da hare ta kasa da kuma jiragen sama na yaki don farautar 'yan boko haram, wadanda sojojin suka ce suna kokarin arcewa..

Wani mazaunin Maiduguri ya shaida wa BBC cewa titunan birnin sun yi fayau, ba kowa sai jami'an tsaro da 'yan kato-da-gora;

Yakin neman zabe

Harin dai ya zo ne kasa ga kwana daya bayan shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya gudanar da yakin neman sake zabensa a birnin, yayin da ake sa ran babban abokin hamayyarsa Janar Muhammadu Buhari ya je birnin ranar Litinin.

Karin bayani