An kama maza masu auren jinsi a Kano

Rabi'u Musa Kwankwaso, Gwamnan Jihar Kano
Image caption Rabi'u Musa Kwankwaso, Gwamnan Jihar Kano

Hukumar Hizbah ta jihar Kano dake arewacin Najeriya ta hana wani biki da aka shirya gudanarwa na auren wasu maza.

Shugaban hukumar, Malam Aminu Daurawa ya ce sun kuma kama mutane da dama da suka halarci bikin.

Lamarin dai ya faru a wani wajen shakatawa da ake kira Hills and Valley dake wajen birnin na Kano.

To sai dai daya daga wadanda ake zargi da shirya yin auren ya musanta, inda ya ce za su yi bikin kewayowar ranar haihuwar sa ne kawai.

Hukumar ta Hizba ta ce, yanzu haka ta shiga yiwa wadannan mutane wa'azi don samun shawo kansu su bar wannan dabi'a.