An kashe mutane da yawa a harin Maiduguri

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan Boko Haram sun lalata garin Baga

Mutane da dama ne suka mutu a sakamakon ba-ta- kashin da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan Boko Haram a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Wani dan jaridar, Bello Dukku wanda ya kirga gawawwakin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa galibin wadanda suka mutu 'yan Boko Haram ne.

A cewarsa daga cikin wadanda suka rasu hadda sojoji 15 da kuma wasu fararen hula, sannan kuma wasu fiye da 50 sun jikkata.

Tuni gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bukaci mazauna jihar ka da su razana sakamakon hare-hare na bayan nan da 'yan Boko Haram suka kai.

Gwamna ya ce daruruwan mutane suna ta shigowa Maiduguri daga garin Monguno wanda ya fada hannun 'yan Boko Haram.

Rahotanni daga Maiduguri na cewa hankali ya fara kwanciya, har Jama'a na ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.