An janye dokar hana fita a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin sun hana 'yan Boko Haram shiga Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dage dokar hana fita da aka sanya a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Kanar Sani Usman, ya aikewa BBC ta ce daga karfe shida na safiyar ranar Litinin mutane za su iya fita daga gidajensu.

A ranar Lahadi ne dai aka sanya dokar hana fitar bayan 'yan kungiyar Boko Haram sun yi yunkurin kwace birnin, koda yake sojoji sun fatattake su.

Sai dai duk da haka 'yan Boko Haram din sun kwace garin Monguno da ke nesa da birnin na Maiduguri.

Gwamnan jihar Kashim Shettima ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram sun yi mummunar barna a garin na Monguno.