'Yan sanda sun kai samame ofishin Amazon

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne karo na biyu da aka kai samame ofisoshin Amazon a Japan

'Yan sandan kasar Japan sun kai samame a ofisoshin kamfanin Amazon a birnin Tokyo, a wani bangare na bincike kan zargin kamfanin da sayar da hotunan lalata da yara.

Bayan an kai samamen, kamfanin Amazon ya ce yana bai wa 'yan sanda hadin kai a binciken da suke yi.

Samamen wani bangare ne na ci gaba da dirar wa mutanen da aka yi amanna suna sayar da littatafai da suka kunshi hotunan cin zarafin yara.

A cikin watan Satumba 2013 ne aka fara dirar wa mutanen, inda aka cafke mutane biyu da aka samu sana sayar da littatafan hotuna ta shafin Amazon.

Samamen da aka kai na ranar 23 ga watan Janairu shi ne ne na biyu da kamfanin Amazon ya fuskanta a Japan.

A watan Nuwamban bara an kai irin samamen a wata cibiyar rarraba kayayyakin kamfanin da ke Kanagawa.

Samamen da 'yan sanda ke kai wa ya zo ne bayan an yi gyare-gyare ga dokokin Japan a cikin watan Yunin bara, inda aka haramta mallakan hotunan cin zarafin yara ta hanyar lalata.

A cikin wata sanarwa, kamfanin Amazon ya ce "mun dauki wannan bincike da muhimmanci kuma muna bada hadin kai".

"Ba ma amincewa da duk kayayyakin da aka haramta mu'amala da su a shafinmu kuma muna amfani da wani tsari da ya ke cire ire-iren kayayyakin nan take daga shafinmu", Amazon ya kara da cewa.