Bikin tunawa da sansanin gwale-gwale a Auschwitz

Image caption Rasha ce ta kubutar da mutane daga sansanin

Wadanda suka tsira daga sansanin gwale-gwale na 'yan Nazi a Auschwitz da ke kasar Poland sun yi bikin cika shekaru 70 da tseratar da su da dakarun Rasha suka yi.

Fiye da mutane miliyan daya ne wadanda yawancinsu yahudawa ne aka kashe tsakanin shekarun 1940 zuwa 1945.

An fara taron ne wanda ya samu halartar manyan shugabannin kasashe da addu'o'i da kade-kaden coci.

An jera furanni a wajan da sansanin yake domin nuna alhini.

Wani tsohon fursuna, Roman Kent, ya bayyana irin yadda masu tsaron Nazi suka tursasa rabuwar iyalai da dama, in da suka azabtar da wasu.

Mista kenta ya kuma yi kira ga shugabannin duniya da su inganta tarihin sansanin saboda 'yan gaba su samu tarihi.