Ana iya aika labarai ta Whatsapp a BBC Hausa

Dakin watsa labarai na BBC
Image caption Dakin watsa labarai na BBC

Sashen Hausa na BBC ya bullo da wani sabon tsari ta yadda mutane za su rika aika labarai daga shafinmu na intanetzuwa manhajar WhatsApp.

Da ka shiga cikin labarin da kake so ka aika ta wayar salularka za ka ga alamun whatapp a kasan labarin sai ka latsa, domin aika labarin ga wanda ka ke so.

Sabon tsarin na daga cikin sauye-sauyen da Sashen Hausa na BBC yake ci gaba da yi a shafinsa na intanet wato www.bbchausa.com

Wannan sabuwar hanyar aike wa da labarai zuwa Whatsapp kari ne ga hanyoyin da kuka saba mu'amala da mu, watau ta Email da Facebook da Twitter da kuma Google +.

Karin bayani