Boko Haram ta kai hari a Michika

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rikicin Boko Haram ya jefa mutane da dama cikin tsaka mai wuya

Rahotanni daga garin Michika na jihar Adamawa a Nigeria na cewa 'yan Boko Haram sun kaddamar da hare-hare a kan wasu kauyuka da ke karamar hukumar.

Bayanai sun nuna cewar ko da yake garin Michika na karkashin ikon Boko Haram, amma dai mayakan kungiyar na yinkurin kwace kauyukan da ke kewaye da garin.

Kungiyar Boko Haram ta hallaka dubban mutane a Nigeria tun daga shekara ta 2009 da ta ayyana yaki da hukumomin Nigeria.

A halin yanzu wasu kananan hukumomi a arewa maso gabashin kasar na karkashin ikon Boko Haram inda ta ke aiwatar da shari'ar Musulunci.