Facebook ya fuskanci matsala

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Facebook ya ce ba masu kutse a intanet ne suka yi masa kutse ba.

Shafin sada zumunta da muhawara na Facebook ya fuskanci matsala a ranar Talatar har ta kai mutane sun kasa bude shi tsawon mintuna 40.

Miliyoyin masu amfani da shafin ne dai suka ce sun kasa bude shi.

Sun kara da cewa sun fuskanci matsalar bude manahajar Instagram wadda ake wallafa hotuna a cikinta.

Jami'an shafin na Facebook sun ce injiniyoyinsu ne suka haifar da matsalar, suna masu karyata zargin da ake yi cewa masu kutse a shafukan intanet ne suka kutsa cikin shafin nasu.

Wata mai magana da yawun kamfanin ta shaida wa BBC cewa,"Jiya da yamma mutane da dama sun fuskanci matsalar shiga shafin Facebook da manhajar Instagram. Hakan ya faru ne saboda matsalar na'urorinmu. Babu abin da ya hada wannan batu da kutsen wasu mutane."

Ta kara da cewa sun yi gaggawar gyara matsalar, tana mai cewa "yanzu kowa zai iya amfani da shafin dari bisa dari."