INEC ta yi taro na karshe gabanin zabe

Image caption INEC na ci gaba da rarraba katina na dindindin

Hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta gudanar da taro na karshe da wakilan jam'iyyu da jami'an tsaro da kuma sauran masu ruwa-da-tsaki gabanin zaben kasar da za a yi a watan Fabrairu.

Dukkanin bangarorin da suka halarci taron sun cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa, da tsare-tsare da suka jibanci zabukan.

Batutuwan da suka cimma matsaya a kai sun hada da yin amfani da katin zabe na dindindin, da na'ura ta tantance katin mai zabe.

Kazalika sun amince kan batun a-kasa-a-tsare-a-raka da kuma yadda 'yan gudun hijira za su yi zabe.